News
Gwamnonin arewacin Kasar nan na neman tallafin noma daga bankin raya Afirka
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnonin yankin arewa maso yammacin kasar nansun gana da shugaban Bankin Raya Afirka (Africa Development Bank – AfDB), inda suka nemi tallafin bankin wajen haɓaka harkokin noma.
Wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar Zamfara ta ce gwamnan jihar, Dauda Lawal. ya nemi bankin ya kafa wata da’irar harkokin noma da masana’antu da zimmar sarrafa amfanin da aka noma a cikin gida.
Majalisar wakilai Za ta Karfafawa Hukumomin Tsaro don Tunkarar Kalubalen Tsaro — Abbas
“Yayin tattaunawar da gwamnonin Zamfara, da Kebbi, da katsina, da Jigawa, da Kano, da Kaduna suka yi da shugaban AfDB Akinwumi Adesina, sun faɗa masa yankunan da suka fi buƙatar tallafi,” in ji sanarwar.
Gwamnonin sun nemi agajin bankin ne don ya tallafa musu wajen daƙile ƙalubalen da suka haɗa da tsaro, da inganta rayuwa, da kuma noma, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ta ƙara da cewa bankin ya nuna sha’awarsa ta tallafa wa jihohin, inda “shugaban bankin ya jinjina wa gwamnonin game da fifita walwalar al’ummarsu”.
An daɗe ana nuna fargaba game da ayyukan ‘yan fashin daji da ke hanawa tare da ƙwace wa manoma amfanin gonarsu a waɗannan jihohi, abin da ka iya jawo ƙarancin abinci a yankin da Najeriya baki ɗaya.
A Wani labarin kuma Majalisar wakilai Za ta Karfafawa Hukumomin Tsaro don Tunkarar Kalubalen Tsaro — Abbas
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
