Connect with us

News

Ana Samun Rahoton Cin Zarafin Mata Sama Da 100 A Kowanne Mako A Jihar Kano  -Amnesty International

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International (AI) ta bayyana cewa sama da mutum 100 ne ake samun rahoton cin zarafin su a kowane mako a jihar Kano.

Babbar Darakta, Women in Media Communication Initiative, Halima Ben Umar, wadda ta bayyana hakan a wani taron manema labarai a Kano da aka shirya, ta ce, “A cikin mako guda sama da mutane 139 ne kungiyara ta kama. Cin zarafi da kuma azabtarwa, wanda ke kira da a dauki matakin gaggawa.”

Jam’iyun APC Da NNPP Sun Karyata Batun Shirya Zanga Zanga A Jihar Kano

Da yake bayyana damuwarsa kan wannan lamarin, daraktan hukumar ta Amnesty International Isa Sanusi, ya ce tuni suka bullo da wani shiri na kare hakkin bil’adama tare da mikawa gwamnatin jihar.

Suleiman Yaradua, malami a tsangayar sadarwa ta Jami’ar Bayero Kano (BUK), ya bayyana muhimmancin ‘yan jarida a matsayin ginshikin al’umma.

Advertisement

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa, taron ya yi tsokaci game da buƙatar haɗin kai, musayar bayanai, da aikin jarida na ƙwararrun don magance take haƙƙin ɗan adam a Najeriya.

Taron ya kuma tattauna sabbin dabaru da sabbin hanyoyin magance cin zarafin kan  ‘yancin yara, tare da kai hari akan al’ummar da basu ji basu gani ba, da kuma yunkurin dawo da ‘yancin fadin albarkacin baki.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending