Connect with us

News

Har Yanzu Akwai Gibin Shinkafa Sama Da Tan Milliyan 2 A Najeriya – Bincike

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Wani sabon rahoto da aka fitar ya nuna yadda ake cigaba da samun karuwar amfani da shinkafa a kasar nan, al’amarin da ya sa ake samun gibin Shinkafara da kimanin tan miliyan biyu a duk shekara.

Wannan ya haifar da karuwar sama da kashi 37 cikin 100 na farashin kayayyakin zuwa yanzu a cikin 2023, a cewar rahoton samar da amfanin gona na ‘AFEX kan Kayayyakin amfanin gona na 2023.

An kashe mutane da dama a iyakar Sudan da Sudan ta Kudu

A cikin rahoton ya zuwa yanzu, Najeriya ta kashe sama da dala biliyan 15 a cikin shekaru 10 da suka gabata domin cimma bukatar shinkafa duk kuwa da yuwuwar kasarnan zata na zama mai fitar da shinkafar kasashen waje.

Sai dai ana sa ran samun karuwar noman shinkafa da kusan kashi 4 cikin dari, sannan kuma za a kara samun karuwar farashin shinkafar da kusan kashi 32 cikin dari.

A wani labarin kuma An kashe mutane da dama a iyakar Sudan da Sudan ta Kudu

Advertisement

JamusReutersCopyright: Reuters

Shugaban Najeriya Bola Tinubu (hagu) na cikin mahalarta taron na birnin BerlinImage caption: Shugaban Najeriya Bola Tinubu (hagu) na cikin mahalarta taron na birnin Berlin

Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi alƙawarin samar da dala biliyan 4.4 nan da 2030 ga shirin samar da makamashi maras gurɓata muhalli tsakanin Tarayyar Turai da ƙasashen Afirka.

Yayin ganawa da ƙasashen Afirka da na ƙungiyar G20 a birnin Berlin ranar Litinin, shugaban ya bayyana aniyar sayo “mafi yawan” makamashin da ƙasarsa ke buƙata daga Afirka.

Shirin zai taiamaka wajen samar da wutar lantarki, da dogaro da kai wajen makamashi, da kuma faɗaɗa kasuwanci a nahiyar Afirka.

An ƙirƙiri ganawar tsakanin ƙasashen Afirka da G20 ne a 2017 da zimmar haɓaka tattalin arzikin Afirka ta hanyar ƙara yawan jari.

Advertisement

Jami’an gwamnatin Jamus na ganin Afirka za ta taimaka wa ƙasarsu, wadda ta fi kowacce girman tattalin arziki a Turai, wajen faɗaɗa hanyoyin samun makamashi, da samun ƙwararrun ma’aikata, da rage yawan baƙin-haure, da kuma cimma muradun kyautata muhalli.

A shekarar da ta gabata, kasuwanci tsakanin Jamus da ƙasashen Afirka ya kai darajar dala biliyan 65.4, wanda wani kaso ne kawai na adadin kasuwancin da ƙasar ke yi da ƙasashen Asiya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending