Connect with us

News

Majalissar Wakilai Na Bincike Kan Yadda Hukumomi Suka Kashe Naira Billiyan 447.6 Lokacin Corona

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Majalisar Wakilai ta yi sammacin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya 83 yayin da ta fara bincike kan zargin almubazzaranci da dukiyar gwamnati da ta kai sama da Naira biliyan 447.6 na COVID-19 daga shekarar 2020 zuwa 2022.

Acewar kasafin kudin ma’aikatu da hukumomi akalla 22 daga cikinsu sun samu kasa da Naira billiyan 447.6 a matsayin kudaden tallafin COVID-19 a cikin 2020 kadai.

Da Gangan Aka Hana Lauyoyinmu Kwafin Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan Kano – NNPP

Hukumomin sun hada da Ma’aikatun Kudi da Lafiya, Asibitin Kasa da Abuja da bangaren Aikin Noma da Sadarwa da Matasa da Wasanni, Harkokin Mata da Ayyukan Jin kai, Hukumar Samar da Aiyuka ta Kasa da kuma hukumar gyran tituna FERMA.

Ma’aikatun za su bayyana a gaban ‘yan majalisar don amsa tambayoyi kan zargin karkatar da kudaden rage radadin COVID-19 da aka raba tsakaninsu don yakar cutar da ta addabi duniya.

Advertisement

A wani labarin kuma Majalissar Wakilai Na Bincike Kan Yadda Hukumomi Suka Kashe Naira Billiyan 447.6 Lokacin Corona

Brazil na fama da matsanancin zafin da ba a taba ganin irin shi ba a wasu sassan ƙasar.

Yanayin zafin ya kai maki 44.8 a ma’aunin celcius a birnin Aracuai, kamar yadda hukumar kula da yanayin ƙasar ta bayyana.

Sauyawar yanayin ya janyo hukumomi sun fitar da gargaɗi a sassa daban-daban na Brazil, wata guda gabanin shigowar lokacin bazara a wasu wuraren.

A ɓangare guda mawakiya Taylor Swift ta soke bikin kalankuwar da ta fara, bayan ɗaya daga cikin ‘yan kallo ta fara rashin lafiya, ta kuma rasu a ranar Juma’a da ta wuce saboda tsananin zafi

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending