News
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya garzaya Gaban kotun koli domin kalubalantar tsige shi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara a kotun koli yana kalubalantar tsige shi da kotun daukaka kara ta yi a makon jiya.
Daily News 24 ta ruwaito cewa Mista Yusuf ya shigar da karar ne a yau Laraba.
Za mu yi ta gwagwarmaya har sai an tabbatar mana da kujerar gwamnanmu – NNPP
A cikin sanarwar daukaka karar da jaridar Daily News 24 ta gani, jam’iyyar Abba Kabir Yusuf ta New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta shigar da karar, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa. (INEC).
Advertisements
