News
Emiefiele Ya Lalata CBN Kafin Ya Barta-Gwamnan CBN Cardoso
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Olayemi Cardoso, gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, ya caccaki magabacinsa, Godwin Emefiele, kan aiwatar da manufofin da suka jefa babban bankin kasar cikin mummunan yanayi a shekarun baya.
Cardoso ya bayyana hakan ne a jawabinsa na ranar Juma’a a cibiyar Chartered Institute of Bankers of Nigeria (CIBN) bikin cika shekaru 50 da kafuwa.
Bashin Dalibai Zai Fara A Watan Janairu Na Sabuwar Shekara -Femi Gbajabiamila
A cewarsa, CBN ya sha fama da gazawa wajen tafiyar da harkokin kamfanoni, da rage cin gashin kan hukumomi, da kaucewa babban aikin da ya kamata, da kuma amfani da kudi ba bisa ka’ida ba.
Ina sane da cewa abubuwan da suka faru a cikin ‘yan shekarun da suka gabata sun jefa CBN cikin mummunan yanayi. Ana iya danganta wadannan batutuwa da abubuwa daban-daban, kamar gazawar tsarin mulki na kamfanoni.
Raguwar cin gashin kan hukumomin babban bankin Najeriya,amfani da kudi ba bisa kaida ba da sauransu.
Kafim yanzu, CBN ya kauce daga muhimman ayyukan da ya kamata ya yi, ya kuma tsunduma cikin harkokin kudi wanda ya kai sama da Naira Tiriliyan 10 a cikin tattalin arzikin kasar ta hanyar wasu tsare-tsare daban-daban da suka hada da noma, sufurin jiragen sama, wutar lantarki, matasa da dai sauransu.
Daily Post ta ruwaito cewa Cardoso, ya yi alkawarin cewa za a magance matsalolin da suka shafi Bankin a karkashin kulawar sa.
Ya ce,a karkashin jagorancina, Babban Bankin Najeriya zai magance wadannan matsalolin. Za mu magance gazawar hukumomi, mu maido da tsarin tafiyar da kamfanoni, ƙarfafa ƙa’idoji, da aiwatar da manufofi masu kyau.
