News
Bashin Dalibai Zai Fara A Watan Janairu Na Sabuwar Shekara -Femi Gbajabiamila
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Bola Tinubu, Femi Gbajabiamila, ya ce an tsara tsarin neman rancen dalibai ta hanyar da babu wata alaka tsakanin masu kula da lamuni da masu cin gajiyar shirin.
Gbajabiamila ya ce ana ci gaba da kokarin ganin an fara shirin a watan Janairun 2024 don tabbatar da cewa daliban Najeriya za su iya samun lamunin don samar da kudirin neman ilimi.
Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Kwace Kujerun ’Yan Majalisar Filato Na PDP 11, Ta Ba APC
Daily Post ta ruwaito cewa Ya yi wannan jawabi ne a Legas ranar Juma’a a lokacin da yake gabatar da lacca mai taken, “Karfafa Matasan Nijeriya Kan Tattalin Arzikin Yau” a wajen taro karo na 35 na Kwalejin Fasaha ta Yaba (YABATECH).
Gbajabiamila ya ce, domin kar a samu wata matsala,masu bukata za su yi amfani da yanar gizo, a tantance su ta hanyar yanar gizo, kuma za su yi la’akari da takardun shaida da suka gabatar.
Ya ce,babu wanda zai bukaci sanin kowa don ya cancanci wannan lamuni domin samun damar wannan tallafin ya zama daidai da gaskiya.
Kwanan nan, Tinubu ya rattaba hannu kan dokar ba da lamuni ga dalibai.
Bayan sanya hannu kan kudirin dokar, shugaban kasar ya ba da tabbacin cewa babu wani dalibi da zai fice daga makarantun gaba da sakandare saboda rashin iya biyan kudinsa.
Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa cibiyoyin ilimi sun samu abubuwan da suka dace don gudanar da ayyukansu na harkar ilimi kama daga kayan aiki,albashi alawus alawus da sauransu.
A wani labarin kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Kwace Kujerun ’Yan Majalisar Filato Na PDP 11, Ta Ba APC
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
