Connect with us

News

Kotu Ta Daure Wani Dan Kasuwa Bisa Laifin Satar Kayan Kanti

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wata kotu a garin Jos na Jihar Filato ta daure wani dan kasuwa mai suna Bashiru Aliya mai shekaru 28 a gidan yari har na tsawon watanni tara bisa samunsa da laifin satar kwali biyu na kayan yaji na kudi Naira 98,500.

Advertisement

Alkalin kotun, Shawomi Bokkos, ya yanke wa Aliyu hukuncin ne bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, kamar yadda Kamfanin Dillancin labarun Nijeriya ya ruwaito.

Gwamnatin Kano ta kori ma’aikata sama da 3,000, waɗanda Ganduje ya ɗauka  

Sai dai Bokkos ya ba shi zabin biyan tarar Naira 20,000 tare da umartar sa da ya biya wata Naira 120,000 a matsayin diyya ga wanda ya kai karar.

Advertisement

Tun da farko, dansanda mai gabatar da kara, Sufeto Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa an kai karar ce a ranar 4 ga watan Agusta a ofishin ‘yansanda na Railway da wanda ya shigar da kara, Moses Agbo.

A cewar NAN, mai gabatar da karar ya ce wanda ake tuhumar ya hada baki da abokinsa, ya kuma ya saci kayan a shagon wanda ya shigar da kara da ke kasuwa.

Advertisement

Gokwat ya ce laifin ya saba wa tanadin kundin hukunta manyan laifuka na Filato.

A wani labarin kuma Gwamnatin Kano ta kori ma’aikata sama da 3,000, waɗanda Ganduje ya ɗauka  

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending