Connect with us

News

Alƙalin Alƙalan Jihar  Kano ya bada belin masu ƙananan laifuka 147

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Alƙalin Alƙalan Jihar Kano, Tijjani Ibrahim-yakasai, ya kafa kwamitin sake bibiyar wani da ke tsare gidan kurkuku, shekaru 18 bayan yanke masa hukuncin guntule masa hannu ɗaya.

Yakasai ya kuma bada belin wasu masu ƙananan laifuka har su 147, a wata sanarwa bayan nazarin cinkoso a gidajen kurkukun Kano biyu, na Kurmawa da na Goron Dutse.

Cece Kucen Mutane Ba Zai Sa Mu Yi Abinda Ba Shi Bane Ba-Alkalin Alkalai

Premium Times ta ruwaito cewa Alƙalin Alƙalan Kano shi ne Babban Mai na Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Shari’ar Muslunci na Jihar Kano.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Hukumar Gidan Kurkukun Jihar Kano ya fitar, Musbahu Ƙofar-Nassarawa, bayyana cewa wannan matakin da Alƙalin Alƙalan ya ɗauka, an yi shi ne domin rage cinkoson ɗaurarru a gidajen kurkukun Kano biyu.

Advertisement

“A shekarun baya, Kotun Shari’ar Muslunci ta Jihar Kano ta yanke hukuncin guntule hannun wani da aka samu da laifin sata.

“Amma yanzu kwamitin da aka kafa zai sake nazarin shekaru 18 da ya yi tsare a gidan kurkuku, ba tare da an zartas da hukuncin a kan sa ba.”

Yakasai ya hori waɗanda ya bada belin na su cewa su riƙa bin doka, kuma su zamo mutanen kirki, nagari, sannan su guji aikata duk wani laifin da ka iya sake kama su a maida sucikin kurkuku.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending