News
Yanzu-Yanzu: Mataimakin Gwamnan Edo Zai Kara Da Ubangidansa A Zaɓen Jihar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gabanin zaben gwamnan jihar Edo a shekarar 2024, mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, ya bayar da sanarwar a hukumance, inda ya bayyana muradin sa na neman tikitin takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party a zaben fidda gwani na jam’iyyar da ke tafe.
Shaibu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin a safiyar ranar Litinin
Abdullahi Abbas Zai Maka Dederi A Kotu Kan Zargin APC Da Murɗe Shari’ar Gwamnan Kano
Philip Shaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a zaben 2024 a karkashin jam’iyyar PDP.
Ya ce ya yi aiki tare da Gwamna Godwin Obaseki a cikin shekaru bakwai da suka gabata wajen kafa harsashin ci gaban jihar Edo.
Shaibu ya yi kira ga jama’a da su ba shi goyon baya wajen ganin ya cimma burinsa na zama gwamnan jihar.
An bukaci mataimakin gwamnan ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamna a Otel din Eterno amma otal din ya soke taron a minti na karshe, inda ya ce Gwamna Obaseki yana da shirin gudanar da taron a lokaci guda.
Obaseki da Shaibu sun yi takun-saka ne a kan takarar gwamna.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
