Connect with us

News

An Bude Kasuwar Barci Bayan Shafe Tsawon Shekara Uku 3 A Kaduna

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Bayan shafe tsawon shekara uku ana gyaran Kasuwar Barci da ke Tudun Wada a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, gwamnatin jihar ta sake bude kasuwar.

Ana iya tuna cewa, tsohon gwamnan jihar, Nasiru El-Rufa’i ne ya rushe kasuwar domin zamanantar da ita.

Yanzu-Yanzu: Mataimakin Gwamnan Edo Zai Kara Da Ubangidansa A Zaɓen Jihar

Sai dai wannan yunƙuri ya fuskanci kalubale, inda ‘yan kasuwar da dama da suka rasa shaguna da jari ke korafin kudin hayar shago da suka ce ya gagare su.

Aminiya ta ruwaito cewa  Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Kabiru Yakubu Jarimi, ya shawarci tsofaffin ’yan kasuwar da su nemi ba’asin shagunansu.

Advertisement

Shugaban wanda ya samu wakilcin Sakataren karamar hukumar, Abdulrahman Yahaya, ya shawarci ‘yan kasuwar da su yi watsi da shawarwarin masu hana su komawa kasuwar.

Ya ce dole ne su koma su nemi hakkin shagunansu tun da sun kasance suna da shaguna a baya a cikin kasuwar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending