News
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Bayyana Shirinta Na Kawar Da Bahaya A Bainar Jama’a A Fadin Jihar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana shirinta na hada kai da duk wata hukumar dake bada tallafi domin kawar da bahaya a bainar jama’a a jihar.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar Yunusa Lade, shine ya bada wannan tabbacin lokacin da wata tawagar asusun bada agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya karkashin jagorancin Misis Theressa Pammer ta ziyarci ofishinsa dake Ilorin babban birnin jihar.
An Bude Kasuwar Barci Bayan Shafe Tsawon Shekara Uku 3 A Kaduna
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta ware kudi naira Miliyan 200 domin samar da bandakuna da sauran abubuwan da za su hana yin bahaya a bainar jama’a. Ya ce ‘yan majalisar, a matakin jiha da na tarayya sun dukufa wajen ganin sun kara kaimi a kokarin da gwamnatin jihar keyi na
A wani labarin kuma An Bude Kasuwar Barci Bayan Shafe Tsawon Shekara Uku 3 A Kaduna
Ƙasar Saliyo ta ɗage dokar takaita zirga-zirga ta sai baba ta gani da ta saka a faɗin ƙasar a ranar Lahadi bayan da wasu sanye da kakin sojoji suka kai hari barikin sojoji da kuma kuma gidajen yari.
Yanzu, dokar hana zirga-zirgar za ta fara aiki daga karfe 9 na dare zuwa 6 na safe agogon ƙasar har sai abin da hali ya yi.
Shugaba Julius Maada Bio, ya yi wa ƴan ƙasar jawabi , inda ya ce an kama yawancin shugabannin da suka kai harin kuma za a tuhume su
Hankula dia sun fara kwanciya a ƙasar.
Mista Bio ya kwatanta al’amarin a matsayin hari kan dimokraɗiyya, sai dai bai bayyana sunayen mutanen ba ko kuma magana kan yunkurin juyin mulki.
Tun da farko a ranar Lahadi, gwamnatin ƙasar ta Saliyo ta ɗora laifi kan wasu sojoji saboda sun yi yunkurin kutsawa cikin barikin.
Ana kyautata zaton cewa waɗanda suka kai harin sun sake wasu furusnoni tare da yin garkuwa da su.
An sake zaɓar Shugaba Bio a watan Yuni, sai dai a watan Agusta aka kama wasu sojoji, inda aka zarge su da makarkashiyar kifar da gwamnati
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
