News
Gwamnatin jihar Jigawa ta sake jaddada dokar takaita zirga-zirgar ababen hawa a Dutse
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Gwamnatin jihar Jigawa ta sake jaddada dokar hana zirga-zirgar babura na kasuwanci a Dutse babban birnin jihar daga wayewar gari zuwa karfe 10 na dare, da sauran ababen hawa bayan karfe 11:59 na dare domin tabbatar da tsaro.
Dokar hana zirga-zirgar dai ta fara aiki ne a lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Mohammed Badaru Abubakar, wanda yanzu ya zama Ministan Tsaro.
CBN Zai Haramta Harkokin Kudi A Asusun Bankin Da Babu BVN Da NIN A 2024
A lokacin da sabuwar gwamnatin Gwamna Umar Namadi ta hau mulki, ta sake duba dokar don taimakawa wajen shawo kan matsalar tsaro a cikin Jihar.
Daily Trust ta rawaito cewa Sai dai mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta sanya matakan da za su ba mutane damar tsallakawa babban birnin jihar tare da basu dama ga wadanda ke cikin mawuyacin hali kamar asibiti.
Wani mazaunin garin Sani Rabi’u ya ce dokar ta yi kyau sosai kuma ya ji dadi domin ba a keta haddi tun da aka fara takurawa.
Sai dai ya ce akwai mutanen da ke da matsalar gaggawa kamar zuwa asibiti, yana mai ba da shawarar cewa jami’an tsaro su kyale irin wadannan mutane bayan sun tabbatar da ikirarinsu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce an hana su ne sakamakon tabarbarewar tsaro da suka kai ga sace babura, da yin garkuwa da mutane , da dai sauran munanan dabi’u, ya ce, “Mun samu nasarori ta fuskar tsaro tun a wancan lokacin, kuma hukumar da gwamnati mai ci ta sabunta dokar ne domin jihar ta ci gaba da zaman lafiya.”
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa a kwanakin baya an yi garkuwa da matan shugaban karamar hukumar Kiyawa, Nasiru Ahmed Kiyawa, da wani mutum daya a Rungumau a karamar hukumar Dutse, daga bisani aka sako su.
