News
Kotu ta yanke wa Sarkin Fulani, Usman daurin rai da rai
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babban kotu dake Ilorin babban birnin jihar Kwara ta yanke wa wani basarake da wasu mutum biyu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan an same su da laifin yin garkuwa da mutane.
Kotun ta tuhumi sarkin Fulani Usman Adamu, kanensa da wani Gidaddo Idris bisa zargin aikata laifin hada baki da yin garkuwa da mutane.
Alkalin kotun Adenike Akinpelu bayan ya yanke hukuncin ya ce abin tashin hankali ne yadda sarakunan gargajiya da aka dorawa nauyin kare rayuka da dukiyoyin jama’a ke cutar da mutane saboda son rai da son duniya.
Akinpelu ya kuma umarci mutanen da su biya wanda suka yi garkuwa da shi naira 600,000 diyyar muzguna masa da suka yi.
Shugaban fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka na jihar Idowu Ayoola ne ya shigar da kara kotu.
Ayoola ya ce Adamu da abokan sa sun yi garkuwa da wani Abubakar Ahmad a shekarar 2022.
Ya ce Adamu ya yi tsawon kwanaki 20 a hannun waɗanda suka kama shi sannan suka sake shi bayan ƴan uwan shi sun biya Naira miliyan daya kudin fansa.
A wani labarin kuma Dan Majalisa Mai Wakiltar karamar hukumar fagge ya gabatar da ko Kensa Bisa Kisan Salisu Player a zauren majalisa
Hukumar MDD mai agaza wa Falasɗinawa ta UNRWA ta ce babu wasu kayan agaji da suka shiga Zirin Gaza tun bayan ƙarewar yarjejeniyar tsagaita wuta ta ɗan lokaci a ranar Juma’a.
Juliette Touma, mai magana da yawun UNRWA, ta faɗa wa BBC cewa: “Abin da muke fargaba shi ne za mu koma inda muke a farkon wannna rikici, lokacin da aka hana shiga da koma Zirin Gaza – wanda har yanzu ake ci gaba da jin raɗaɗinsa.”
Ta ce akwai ƙoƙarin da ake yi na ci gaba da kai kayan agajin, kuma ta yi kiran a tsagaita wuta.
“Yanzu muna dab da afkawa cikin bala’in da ɗan’adam ya ƙiƙira a Gaza,” a cewar Touma.
-
News1 day ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
