News
Gobara ta kone shaguna a jihar Jigawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Akalla shaguna uku da wasu kayayyaki masu daraja na miliyoyin naira ne suka kone a ranar Juma’a sakamakon gobara da ta tashi a unguwar kasuwar Bakin da ke karamar hukumar Hadejia a jihar Jigawa.
DSC Adamu Shehu, kakakin hukumar tsaron farin kaya ta kasa (NSCDC) a jihar ya tabbatar da faruwar lamarin a Dutse ranar Asabar kamar yanda Jaridar Daily News24 ta ruwaito
Shehu ya ce gobarar ta kone kantuna uku da rumfa da wani bangare na wani masallaci a yankin
“A ranar Juma’a da misalin karfe 10:30 na rana, ofishin hukumar NSCDC reshen Hadejia ya samu kiran wayar tarho game da gobarar da ta tashi a rukunin shagunan Na Malam Zangi da ke Bakin Kasuwa, babbar kasuwar Hadejia.
“Nan da nan aka tura tawagar jami’an bayar da agajin gaggawa zuwa wurin domin kashe gobarar tare da ceto dukiyoyin da ba a kone ba tare da kiyaye sata.
Ya bayyana cewa har yanzu ba a gano takamammen hanyar da wutar ta tashi ba.
Kakakin hukumar NSCDC, ya ce wanda lamarin ya faru a kan idonsa, ya yi ikirarin cewa gobarar ta tashi ne daga wata wutar lantarki da ke kusa da daya daga cikin shagunan.
Shehu ya ce, an kashe gobarar ne da hadin gwiwar jami’an NSCDC, hukumar kashe gobara, da mazauna yankin.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
