Connect with us

News

Gwamnatin jihar Ogun ta bayyana cewa za ta kwace duk gidan da babu banɗaki a jihar.

Published

on

Advertisements
ads

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Gwamnatin jihar Ogun ta bayyana cewa za ta kwace duk gidan da babu banɗaki a jihar.

Gwamnati ta yi wannan gargaɗi ne domin kawo ƙarshen matsalar yin bahaya a waje a jihar.

Turkiyya ta kwashe ‘yan kasarta daga Gaza a yayin da Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta

Wannan gargaɗi na kunshe a wata sanarwa da kwamishinan muhalli na jihar Ola Oresanya ya fitar a makon jiya a garin Abeokuta.

“Daga yanzu gwamnati za ta kwace gidajen da a su da banɗaki kuma ba su gina guda ba. Sannan kuma da gidan da ba bu banɗaki kwatakwata.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa Oresanya ya ce tun ba yanzu ba gwamnati ta gargadi masu gidaje kan gina bandaki a gidajen su tare da basu wa’adi domin ganin sun yi hakan.

Ba kawai kama kwace gida ba, shi kansa mai gidan za a kama shi.

A wani labarin kuma Turkiyya ta kwashe ‘yan kasarta daga Gaza a yayin da Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta

Shugaban rundunar sojin Isra’ila ya ce sun fara kai hare hare ta kasa zuwa kudancin Gaza, bayan kawo karshen yarjejeniyar da aka cimma ta tsawon mako guda.

Janar Herzi Halevi, ya shaida wa dakarunsu a kudancin Isra’ila cewa hare haren kada su gaza wadanda suke kai wa kudancin Gazan.

Wakilin BBC ya ce ana lugudan wutar makamin atilari da kuma kai hare hare ta sama a kudancin Gaza tun bayan da yarjejeniyar tsagaitar wutar da aka cimma ta zo karshe a ranar Juma’a.

Advertisement

Kazalika ana ci gaba da kai hare haren bama bamai a Khan Yunis da Rafah.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending