News
Turkiyya ta kwashe ‘yan kasarta daga Gaza a yayin da Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta

DAGA UMMAR IBRAHIM HOTORO
‘Yan kasar Turkiyya da iyalansu wadanda aka kwaso daga Gaza sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa yankin sun isa Istanbul daga Masar.
Trt Afirka ta ruwaito cewa Jirgin saman Turkish Airlines dauke da ‘yan kasar Turkiyys 142 wadanda suka tsallaka Masar ta Mashigar Rafah sun sauka a filin jirgin saman Istanbul Dda sanyin safiyar Litinin bayan ya taso daga filin jirgin saman kasa da kasa na birnin Alkahira.
Kungiyar SERAP Ta Nemi Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar Gina Wa Shettima Gidan Naira Biliyan 15
Jami’an Ma’aikatar Harkokin Waje Turkiyya da na Hukumar Kiyaye Aukuwar Bala’i (AFDA) ne suka tarbe su.
Wasu daga cikinsu sun yi ta hawaye a yayin da suka sauka daga jirgi.
Ranar 19 ga watan Nuwamba, Turkiyya ta kwaso ‘yan kasarta 42 daga Gaza.
Isra’ila ta ci gaba da kai are-hare Gaza ranar Juma’ar da ta gabata bayan karewar wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da kungiyar Hamas ta Falasdinawa.
Hare-haren da ta kaddamar ranar 7 ga watan Oktoba sun kashe Falasdinawa akalla 15,500, galibinsu kananan yara da mata bayan harin ba-zata da Hamas ta kai mata.
A wani labarin kuma Dakaru sojojin sun kashe ƴan ta’adda 180 sun kama 204 cikin mako guda
Shugaban rundunar sojin Isra’ila ya ce sun fara kai hare hare ta kasa zuwa kudancin Gaza, bayan kawo karshen yarjejeniyar da aka cimma ta tsawon mako guda.
Janar Herzi Halevi, ya shaida wa dakarunsu a kudancin Isra’ila cewa hare haren kada su gaza wadanda suke kai wa kudancin Gazan.
Wakilin BBC ya ce ana lugudan wutar makamin atilari da kuma kai hare hare ta sama a kudancin Gaza tun bayan da yarjejeniyar tsagaitar wutar da aka cimma ta zo karshe a ranar Juma’a.
Kazalika ana ci gaba da kai hare haren bama bamai a Khan Yunis da Rafah.
