Connect with us

News

Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum a  hanyar jihar Kaduna zuwa Abuja

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum 16 tare da jikkatawa su 17 a jihar Kaduna.

Rahotonni sun ambato kwadandan Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadurra ta Najeriya mai lura da jihar Kabir Nadabo na cewa hatsarin ya auku ne a ƙauyen Audu Jhangon da ke kan babban titin Abuja zuwa Kaduna

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf Ya Nada Sabuwar Shugabar Kwalejin Aikin Jinya Da Ungozoma

Ya ce hatsarin ya auku ne da asubahin ranar Lahadi lokacin da wata babar motar daf, ta ƙwace wa direbanta tare da faɗa cikin rami.

“Rahotonnin farko da muka samu sun nuna cewa direban na tsakiyar gudun wuce kima”, in ji Nadabo.

Advertisement

Ya ce tuni jami’an hukuar suka kai ɗauki domin tseratar da mutanen da lamarin ya shafa.

“Hatsarin ya rutsa da mutum 65, inda mutum 27 suka jikkata, yayin da 16 suka mutu”.

Ya ce tuni aka kai waɗanda suka jikkata asibiti domin ba su kulawar gaggawa.

Bbc ta ruwaito cewa Hatsarin mota dai wata babbar matsala ce a titunan Najeriya, da ke laƙume rayukan ‘yan ƙasar masu yawan gaske a kowace shekara.

Matsalar da masana ke alaƙantawa da rashin kyawun titunan ƙasar, da kuma rashin bin ƙa’idojin tuki daga ɓangaren direbobi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending