News
Yadda Gwamna Katsina Dikko Raɗɗa ya fafata gumurzu da ‘yan bindiga a dajin Safana
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Katsina Dikko Raɗɗa, ya yi kukan-kura da ƙumumuwar jan gamayyar rundunar jami’an tsaro, inda suka fafata fatattakar ‘yan ta’adda a yankin Zakka, ciki Ƙaramar Hukumar Safana.
Cikin wata sanarwar da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna Raɗɗa, Kaula Mohammed ya fitar a ranar Lahadi, ya ce rundunar barde Dikko Raɗɗa ta samu nasarar ceto wani magidanci mai shekaru 33 da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da shi.
Tawagar ‘Yan Wasan Super Eagles Ta Nijeriya Ta Koma Ta 44 A Fagen Kwallon Kafa A Duniya
Mohammed ya ce Gwamna Raɗɗa ya je Safana ne domin ƙaddamar da wani aikin rabon kayan inganta rayuwar al’umma, wanda Maitaimakin Kakakin Majalisar Jihar Katsina, Abduljalal Runka ya ɗauki nauyi.
Premium Times ta ruwaito cewa Ana wurin taron ƙaddamar da shirin ne, sai jami’an tsaro suka samu kiran neman ceton gaggawa cewa ga ‘yan bindiga can na shirin afkawa ƙauyen Zakka.
Nan da nan sai Gwamna ya zabura, ya tsayar da aikin ƙaddamar da shirin inganta rayuwar al’umma, shi da wasu ‘yan tawagar sa suka shiga cikin zugar gamayyar jami’an tsaron da suka haɗa da ‘yan sanda, Sojojin Sama Dakarun Operation Hadarin Daji da Sojojin Ƙasa da kuma ‘yan sakai na Security Watch Corps.
“Sun fafata da ‘yan bindiga a Dajin Zakka kafin su kai ga hawa tsauni.
” An ceto wani magidanci mai shekaru 33 bayan an yi gumurzun da ya kai tilas ‘yan bindigar suka arce, bayan mintina 30.
Sanarwar dai ta ce ba a kashe ɗan bindiga ko ɗaya ba.
Daga nan Gwamna Raɗɗa ya bada umarnin a kai wanda aka ceto ɗin asibiti, saboda ‘yan bindiga sun harbe shi a ƙafa, kafin a samu nasarar kuɓutar da shi.
