News
Daga Karshe Gwamna Akerodolu Ya Amince Da Baiwa Mataimakinsa Rikon Kwarya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya bukaci mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, da ya dauki nauyinsa a matsayin mukaddashin gwamnan jahar Ondo yayin da ya tafi hutun jinya daga ranar Laraba.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin gwamnan, Richard Olatunde ya fitar ranar Talata.
Harajin da ake karɓa daga kamfanoni ya ƙaru da kashi 116% – Hukumar NBS
Sanarwar ta ce gwamnan, wanda ke fama da rashin lafiya tun daga watan Janairu,zai ba da fifiko ga lafiyarsa tare da tabbatar da samun cikakkiyar lafiya kafin ya ci gaba da aikinsa.
Wasu sassan sanarwar sun ce za mika wa majalisar dokokin jahar wata wasika ta hukuma dangane da hutun jinya da sanarwar mika mulki bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya.
A matsayinsa na Babban Lauyan Najeriya kuma dan Najeriya da ake girmama dokokin kasa Gwamna Akeredolu ya dade yana kyamar mika ragamar mulki ga mataimakinsa a lokacin hutun da yake yi na shekara.
Hakan yasa wani lokaci can baya shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kira wani taro tareda mataimakin gwamna da kuma wakilan gwamna Akerodolu inda ya baiwa mataimakin gwamna shawarar cewa ya cigaba da hakuri da matsayinsa na mataimaki har zuwa lokacin da gwamnan zai samu lafiya.
-
News1 day ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
