Connect with us

News

Rundunar Ƴan Sanda Sun Kama Masu Satar Mota A Jihar  Jigawa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta damƙe wata ƙungiyar masu satar motoci. Rundunar 2IC mai magana da yawun rundunar, ASP Abubakar Isah, shi ne ya sanar da haka ga manema labarai a garin Dutse a yau Talata, 12 ga watan Disamba, 2023.

Ya ce kuma rundunar ta yi nasarar ƙwato motoci 3 yayin kamen.

Najeriya Za Ta Tura Jirage Marasa Matuka A Kan Iyakokin Kasar 

A cewarsa “A ranar 19/11/2023 wani Dr Abdullahi Dogo na ƙaramar hukumar GRA Hadejia, ya kawo rahoto ofishin ƴan sanda na Dutse cewa, ya ajiye motarsa ƙirarToyota Corolla mai lamba KHS.96 AA JIGAWA Mai kalar launin Toka a kasuwar Ƴantifa ƙaramar hukumar Dutse a ciki akwai HP Kwamfuta guda ɗaya, iPad ɗaya, jakunkunan kayan sawa guda biyu,hita ɗaya, hula, takalmi, ya shiga kasuwa siya abinci, ko da ya dawo ya tarar motar sa ta yiɓatan damo.”

Da Samun rahoton ƴan sandan da ke aiki da shiyyar Dutse suka bazama inda nan take suka ziyarci wurin .

Advertisement

Mai magana da yawun rundunar ya ƙara da cewa bisa ga bayanan da suka samu a ranar 21/11/2023 an gano ƙirar wannan motar da ake cigiya motFAW VITA mai rijista mai lamba KWL 274 AS lambar Abuja, inda aka gano ta a wurin ajiye motoci a birnin Dutse.

Daily Trust ta rawaito cewa Hukumar ta 2IC ta ce bisa umarnin jami’in ƴan sanda na shiyyar Dutse, rrundunarƴan sandan ta dira yankin, inda ta yi nasarar kama Abdullahi Sani 28yrs of Mashi LGA Katsina State; da Faruk Adamu mai shekaru 29 a karamar hukumar Keffi jihar Nasarawa inda nan take aka tafi dasu ofishin ƴan sanda don ansa tambayoyi

A wani labarin kuma Najeriya Za Ta Tura Jirage Marasa Matuka A Kan Iyakokin Kasar 

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending