Connect with us

Politics

Tsohon shugaban APC Abdullahi Adamu ya yanke shawarar janyewa daga lamuran siyasa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Tsoho Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya ce ya yanke shawarar janyewa daga lamuran siyasa saboda ya fuskanci yana samun damuwa da lamuran siyasa babu gaira babu dalili.

Sanata Adamu ya bayyana haka ne a ranar Asabar a garin Lafiya yayin wani bikin ƙaddamar da wani littafi da aka yi wa take da “Gwamnati mai ci gaba: nuna nasarorin da Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya samau daga 2019 zuwa 2023,” wanda Abdullahi Tanimu ya rubuta.

Kwai Alƙalai, Ƴan Majalisa da manyan jami’an gwamnati dake ɗirka sata – ICPC

Da yake tsokaci kan littafin Abdullahi Adamu ya yaba wa marubucin tare da shawartar ‘yan jihar su ci gaba da baiwa gwamnati goyon baya domin ci gaba da ayyukan raya ƙasa.

BBC ta ruwaito cewa Ya ce “Ba wai ritaya kawai na yi ba, na janye hannuna daga lamuran siyasa. na ci ina samun matsala da siyasa da lamuranta a ‘yan kwanakin nan.

Advertisement

“Kp gafarce ni, ba zan iya ƙara cewa komai ba dangane da siyasa bayan neman haɗin kai da zan so ku ci gaba da baiwa gwamnati.

“Yana buƙatar duk taimakonku da addu’o’inku domin nasararsa,” in ji Adamu.

 

 

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending