Connect with us

News

Kotu Ta Daura Auren Wasu Masoya A Jigawa, Bayan Mahaifin Amarya Yace Bai Gamsu Da Akidar Ango Ba

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Alkalin kotun shari’ar musulunci dake zama a Garun Gabas, ƙaramar hukumar Malam Madori, Mallam Muhammadu Yaba Ibrahim ya daura auren wasu masoya, bayan mahaifin amarya ya ki amincewa da auren a mintunan karshe, sakamakon bincike da ya bayyana cewa angon ba mabiyin mazahabar da ya aminta da ita bane.

Tun da fari dai mahaifin yarinya Mallam Muhammadu Sabiu Mallam Madori ya sanya ranar asabat 16 ga watan Desemba domin daurin auren.

Riƙe katin rigakafi zai inganta bayanan kiwon lafiya – UNICEF

Wannan yasa ango ya saki jiki har ya aike da lefe tare da cika dukkan sharudan alada, kwatsam sai sanarwar soke auren ta bujiro daga mahaifin Amarya.

Sabawa Radiyo ta ruwaito cewa Wannan mataki da Mallam Sabiu ya dauka ya taba zuciyar gidan maza da dangin mahaifiyar yarinyar.

Bayanan da Sawaba radio ta samu sun nuna cewa Amaryar da ake wannan takaddama akanta ta taso ne a hannun dangin mahaifiya tun bayan rasuwar mahaifiyarta.

Advertisement

Fatima sun kwashe kusan watanni 14 suna soyayya da Haruna Sani Garun Gabas.

Wannan yasa yar uwar mahaifiyar Fatima shigar da korafi gaban mai sharia Mallam Muhammadu Yaba Ibrahim, Wanda bayan nazarta da saurarar dukkan bangarorin yayi tawassali da hujjoji daga Alqurani da shari’ar musulunci ya daura auren.

Kuma bayan daurin auren ne angon Haruna Sani ya tabbatarwa Sawaba Radio cewar “In Sha Allahu za’a rike Amarya da amana dai-dai gwargwago, kuma wannan kaddarar ce zata iya faruwa da kowa”.

Haka mahaifin Angon ya bayyana cewa zasu tabbatar wannan sabani bai zama silar taba zumuncin Fatima da mahaifinta ba.

A wani labarin kuma Riƙe katin rigakafi zai inganta bayanan kiwon lafiya – UNICEF

Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.

Advertisement

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending