Connect with us

News

Riƙe katin rigakafi zai inganta bayanan kiwon lafiya – UNICEF

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

 

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ba da tabbacin cewa a shirye yake ya fara wayar da kan jama’a kan muhimmancin rike katin allurar rigakafin yara.

 

Jami’ar kula da harkokin a yankin Kano, Rahma R. Farha ta bayyana hakan a yayin taron tattaunawa na kwana daya da masu ruwa da tsaki daga jihohin Kano, Jigawa da Katsina kan batun rike katunan rigakafi da Hukumar Wayar da kan Jama’a ta Kasa (NOA) tare da hadin gwiwar Asusun kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) suka shirya.

Gwamnatin nmu Zata tabbatar da Adalci a tsakanin Duka Addinai Dake Jahar Kaduna.

Mista Farha, wanda Mista Ogu Enemaku ya wakilta, ya ce matakin rike katin abu ne mai matukar muhimmanci bai yi muni ba, ya kara da cewa suna son kowane yaro ko babba idan an yi masa allurar rigakafin ya rike katinsa.

Advertisement

 

“Katunan rigakafi bayanan kiwon lafiya ne waɗanda bai dace a lalata su ba. Da zarar an yi wa kowa allurar rigakafi kuma an ba shi katinsa, ya kamata ya riƙe katin don amfani a gaba”, a cewar Mista Enemaku.

 

Ya yi nuni da cewa, alkaluman wannan batu sun sha banban daga wannan jiha zuwa waccan, ko kuma daga wannan karamar hukuma zuwa waccan, amma gaba daya ya kai matsakaicin matsayi a lokaci guda.

 

”Bayanan da aka gabatar mana daga Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta Jihar Kano sun nuna cewa, a kowace karamar hukuma akwai adadin kudin da ake ajiyewa, amma akwai bukatar a inganta tsarin. Duk wani yaro ko babba da aka yi wa allurar rigakafin ya kamata a ajiye masa katinsa, kada a batar ko a bari a sace, don abu ne mai matukar muhimmanci na tarihi”, Mista Enemaku ya kara da cewa.

Advertisement

 

A jawabinsa na maraba, Ko’odinetan NOA reshen jihar Kano, Alhaji Salisu Uzairu Kutama, ya ce taron an yi shi ne da nufin ganin an fadakar da al’umma muhimmancin rike katin rigakafi.

 

Alhaji Salisu Uzairu Kutama ya kuma yi kira ga jama’a da su sani cewa duk abin da gwamnati za ta kawo na amfanin kansu ne.

l

“Rike katin yana da matukar muhimmanci. Na yi kira ga iyaye maza da mata a duk lokacin da aka yi wa ‘ya’yansu allurar rigakafi, ya kamata a kiyaye katin rigakafin da kyau”. Alhaji Kutama ya ce.

Advertisement

 

Da yake jawabi tun da farko, Jami’in Wayar da Kan al’umma na Hukumar Wayar da lafiya matakin farko na jihar Kano, Malam Ado Sanda, ya yi nuni da cewa katin rigakafin ya kunshi bayanan ranar haihuwa, gari ko kauye, da adadin allurai na kowane yaro don samun bayanan da ake samu a kowane cibiyar kiwon lafiya a fadin jihar.

 

Malam Ado Sanda ya kara da cewa, bisa sabon tsarin da Hukumar kula da Lafiya Matakin Farko ta Kasa ta fitar, sabon katin zai kunshi matakai 3; daya na yaro, wani na kayan aiki, sannan kuma na karshe na sarkin gargajiya a yankin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending