Connect with us

News

Mai Bincike Akan Bankin CBN Ya Bankado Asusun 593 Na Kasashen Ketare Masu Alaka Da Emefiele

Published

on

Tsohon Gwamnan Babban Bankin CBN, Godwin Emefiele

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Tsohon Gwamnan Babban Bankin CBN, Godwin Emefiele, ya sanya biliyoyin Naira a asusun bankuna 593 na kasashen Amurka da Ingila da China ba bisa ka’ida ba, kuma ba tare da amincewar kwamitin gudanarwa na bankin ba.

Wani jami’in bincike na musamman kan CBN da wasu ma’aikatu, Jim Obaze, ya gano cewa tsohon gwamnan na CBN ya ajiye kudi fam billiyan 543 da milliyan 482 da 213 a asusun ajiya a bankunan kasar Birtaniya kadai ba tare da izini ba.

Advertisement

Sakamakon mai taimakon mabuƙaci tun a duniya yake zuwa -Malam Ja’afar

Obaze ya mika rahotonsa na karshe ga shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba inda ya yi ikirarin cewa ya gano kudaden da Emefiele ya zuba ba tare da izini ba a wasu asusun banki guda 593 na kasashen waje a lokacin da yake rike da mukamin.

Lauyoyin Emefiele bisa jagorancin, Mathew Bukkaa, har yanzu bai mayar da martani kan wannan zargi ba yayin da jaridun Punch ta tuntube su har zuwa lokacin gabatar da rahoton a safiyar yau.

Advertisement

A wani labarin kuma Sakamakon mai taimakon mabuƙaci tun a duniya yake zuwa -Malam Ja’afar

Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.

Advertisement

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Advertisement

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Advertisement

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending