Connect with us

News

Sauya Launin Naira da Emefiele ya yi, zamba da harƙalla ce kawai – Mai Binciken CBN

Published

on

DAGA  KABIRUBASIRU FULATAN 

Mai Binciken CBN na Musamman, Obazee, ya bayyana a cikin rahoton binciken da ya gudanar cewa shirin sauya launin kuɗin da tsohon Gwamnan CBN, Goodwin Emefiele ya bijiro da shi, harƙalla ce kwai da zuma tantagaryar zamba.

Advertisement

Ya ce shirin ba a nemi amincewar Hukumar Gudanarwar CBN ba, kuma ba a nemi amincewa a rubuce daga shugaban lokacin ba, Muhammadu Buhari.

Yan Sanda Sun Cafke Mata Da Mijinta Tareda Makwabcinsu Bisa Zargin Su Da Aikata Laifin Kisan Kai A Kano 

Ya ce hakan kuwa an kauce wa Sashe na 19 (1) na Dokar CBN, ta 2007.

Advertisement

“Kawai wata maƙarƙashiya ce Emefiele ya shirya domin damfarar ‘yan Najeriya, musamman manyan ‘yan siyasa. Kuma Emefiele ne ya shirya wannan zambar, shi da mataimakin sa a wancan lokacin, mai suna Folashodun Shonubi.

 

Advertisement

“Emefiele da Shinubi sun shirya zambar sauya launin kuɗi don su hana wasu manyan ‘yan siyasa kasa cimma burin su. To amma sai abin ya zama masifa da bala’in ƙuncin rayuwa ga ɗaukacin ‘yan Najeriya kamr yanda Jaridar premium Times ta ruwaito 

Obazee ya ce CBN ya yi sabbin kuɗaɗen na N200, N500 da N1,000, kuma Naira bilyan 61.5 ya kashe wajen buga kuɗaɗen, waɗanda ya biya Naira biliyan 31.8 ga ɗan kwangilar. Kuma Naira biliyan 769,562 kaɗai na sabbin kuɗaɗen aka buga.

Advertisement

“Emefiele ya kwashi Naira 1,727,500,000 wai ya biya kuɗin lauyoyin biyo bayan shigar da CBN ƙara da aka yi ta yi, bayan ya sauya launin kuɗi.” Haka Obasee ya bayyana a cikin rahoton sa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending