News
Rundunar Ƴan Sanda Ta Kama Waɗanda Ake Zargi Da Satar Shanu A Kaduna
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa jami’anta sun kama wasu mutane biyar da ake zargin barayin shanu ne tare da kwato shanu huɗu daga gurin wadanda ake zargin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Kaduna.
Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin yawan kwallaye a 2023 a duniya
Ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a garin Tafa da ke ƙaramar hukumar Kagarko a jihar.
Wikki Time ta ruwaito cewa “A ranar 30 ga Disamba, shekarar bara ne jami’an mu da hadin gwiwar jami’an Rundunar tsaro ta JTF su ka kama wani matashi ɗan kimanin shekaru 20 da ake zargi da aikata satar shanu”
Haka kuma ASP Mansir Hassan ya ce an samu wanda ake zargin da shanu guda hudu da ake zargin na sata ne.
Ya kara da cewa bayan ƴan sanda sun gudanar da bincike kan wanda ake zargin, ya amsa cewa manajan wata gona da ke garin Sabon Wuse ya ba shi amanar kiwon shanun.
“Babban wanda ake zargin ya ce sun hada baki ne da sauran mutane hudun da ake zargin sun sayar da shanun da suka sace,” inji shi.
Hassan ya ce wadanda ake zargin dukkansu suna hannun ‘yan sanda domin ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da su a gaban kotu idan sun kammala bincike.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
