Connect with us

News

Kotu Ta Umarci Gwamnati Tarraya Ta Biya Emefiele Diyyar N100m

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Kotu ta umarci Gwamnatin Tarayya da Hukumar yaki da Masu Karya Tattalin Aziki (EFCC) su biya tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele diyyar Naira miliyan 100 kan tauye hakkinsa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, cewa Mai shari’a Olukayode Adeniyi na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya ne ya ba da umarnin a ranar Litinin, inda ya kuma hana gwamnati sake tsare Emfiele ba tare da samun izinin yin hakan daga kotu ba.

Advertisement

Za’a Hana Masu Layin Glo Kiran MTN — Hukumar NCC

Emefiele wanda ke fuskantar shari’a kan badakalar kudi, ya maka Gwamnatin Tarayya, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) da EFCC a kotu ne, kan tauye masa hakkokinsa na rayuwa, walwala, ’yancin kansa, da kuma na damar bayani.

Tsohon gwamnan CBN din ya bukaci alkalin ya umarce su su biya shi diyyar Naira biliyan daya kan tauye masa hakkokinsa.

Advertisement

Emefiele ya tunatar da kotu cewa tsare shi da EFCC da gwamnati suka yi daga ranar 10 ga Yuni, 2023 zuwa 26 ga Oktoba, 2023 ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba haramun ne.

Ya kara da cewa saba umarnin kotu da dama na a sake shi da wadanda ake karan suka yi, take hakkinsa ne na rayuwa, ’yancin kai da walwala, wadanda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da kuma kundin tsarin mulkin dan Adam na Afrika suka tabbatar.

Advertisement

A wani labarin kuma Za’a Hana Masu Layin Glo Kiran MTN — Hukumar NCC

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending