Connect with us

News

Bamu da wani Farfesan bogi a Jami’ar Bayero – Shugaban Jami’ar.

Published

on

DAGA AISHA MUHAMMAD BASHIR

 

Jami’ar Bayero da ke kano,ta musanta rahoton da ake yadawa na cewar an gano farfesoshin bogi har guda 20 a jami’ar.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa jami’ar ta musanta labari ne ta cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, me dauke da sa hannun Shugaban Jamil’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas.

Sanarwar tace ta kula da yadda ake yada wata sanarwar bogi a kafafan sada zumunta, wadda ke cewa an gano farfesa guda 100 na bogi dake aiki a Jami’oin Najeriya.

A saboda haka ba tare da wata shakka ba,muke sanar daku cewa waccan sanarwa da ake yadawa, ba komai bace illa mara tushe, wadda wasu suka kirkira domin taba martabar jami’ar.

Advertisement

Haka kuma shugaban jami’ar yayi bitar yadda hukumar dake kula da jami’oin kasar, ta tabbatar da cewa waccan sanarwa ta bogi ce.

Sanarwar ta kara da cewa ”babu yadda za’ai a sami irin wannan lamari a jami’ar Bayero, duba da yadda muke cikin manyan jami’oin da suke bada ingantaccen ilimi, kamar yadda masu kididdiga akan jami’oin duniya suka tabbatar”.

A kokarin kauda shakku daga zukatan Al’umma, Jami’ar tace ko a baya-bayan nan ta zama ta biyar a sahun jami’oi masu inganci a najeriya, a fannin bincike,bada horo dama ingantaccen tsarin koyo da koyarwa.

 

Haka kuma Jami’ar ta zama ta biyu a Najeriya a bangaren wadanda tsarukan su yayi dai -dai da na kasashen duniya, wanda kuma hakan ya faru ne a sakamakon ingantaccen ilimin dama samar da Daliban da sukayi zarra a tsakanin sa’oinsu.

A karshe Jami’ar tayi fatan Al’umma zasu yi watsi da waccan sanarwa da ake yadawa.

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending