Connect with us

News

Dalilan da suka sa CBN ya ƙwace Bankin Union, Keystone da Polaris, ya naɗa masu sabbin daraktoci

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ruguza hukumomin gudanarwar Bankin Union, Polaris da Keystone a ranar Laraba, tare da sauke shugabannin bankunan, Babban Bankin Najeriya, CBN ya naɗa wa bankunan sabbin shugabanni.

Advertisement

Cikin wata sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na CBN, Makama Sidi Alli ya fitar, an naɗa Yetunde Oni matsayin Shugaba kuma Manajan Daraktan Union Bank, shi kuma Mannir Ubale Ringim Babban Darakta.

Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Ziyarci Wace Aka Sacewa Jariri Awa 3 Da Haihuwarsa A Asibiti

Shi kuma Bankin Keystone an naɗa masa Hassan Imam Shugaba kuma Manajan Darakta, yayin da Chioma A. Mang aka naɗa ta Babbar Darakta.

Advertisement

Bankin Polaris an naɗa masa Lawal Mudassir Omokayode Akintola Manajan Darakta, sai Onyeka Ofikulu Babbar Darakta.

CBN ya ce naɗin na su ya fara aiki nan take.

Advertisement

Sai dai CBN Bai bayar da tarihin waɗanda aka naɗa ɗin ba. Amma binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa Yetunde Oni da aka naɗa shugabancin Union Bank, an ɗauko ta ne daga shugabancin Standard Chartered Bank na Saliyo.

Shi kuma Hassan Imam na Keystone Babban Darakta ne a Fedility Bank.

Advertisement

Mudassir Lawal kuma da aka naɗa Bankin Polaris, Babban Darakta ne a Sterling Bank.

CBN ta rushe shugabannin Union Bank, Polaris da Keystone saboda ƙin bin dokar Tsarin Hada-hadar Kuɗaɗe Sashe na 12(c), (f), (g), (h) na Doka ta 2020.

Advertisement

Sauran dalilan ƙwace bankunan sun haɗa da shiga harƙallar da ke kawo barazana ga tsarin hada-hadar kuɗaɗe.

A wani labarin kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Ziyarci Wace Aka Sacewa Jariri Awa 3 Da Haihuwarsa A Asibiti

Advertisement

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

Advertisement

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

Advertisement

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Advertisement

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending