News
SERAP ta bukaci Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas da su rage kasafin kudin Majalisar Tarayya na 2024 na Naira biliyan 344.85.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kungiyar SERAP mai fafutukar Kare Hakkokin Tattalin Arziki da tabbatar da demokradiyya, ta bukaci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas da su rage kasafin kudin Majalisar Tarayya na 2024 na Naira biliyan 344.85.
Kolawole Oluwadare, Mataimakin Daraktan SERAP ne ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
A cewar SERAP, kiran ya zama dole ne biyo bayan yanayin tattalin arzikin da kasar nan ke ciki da kuma bukatar rage tsadar harkokin mulki.
SERAP ta yi zargin karin kasafin kudin 2024 ba bisa ka’ida ba Majalisar Dokoki ta Kasa ta yi.
Kungiyar ta ce ya kamata Majalisar Dokoki ta kasa ta nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da wani sabon kudiri na karin kasafin kudi domin nuna ragi na kasafin kudin Majalisar.
“Karuwar da ‘yan majalisar suka yi ba bisa ka’ida ba na kason kasafin kudinsu idan ba a rage shi ba zai haifar da gagarumin sakamako na kasafin kudi da kuma kara ta’azzara matsalar basussuka a kasar.
“SERAP na rokon ku da ku fayyace dalilin da ya sa aka ware Naira miliyan 225 na Majalisar Dokoki ta E-Library da kuma Naira biliyan 3 don sayen litattafai na Laburare na Majalisar yayin da ‘Take-off Grant’ na dakin karatu na Majalisar ya kai Naira biliyan 12.1.
“Kasafin kudi Naira biliyan 344.48 da ‘yan majalisar dokokin kasar suka yi, wani abu ne da ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
“Kamar yadda muka samu, majalisar ta kara kason nata a kasafin kudin 2024 zuwa Naira biliyan 344.48. Sabon kasafin kasafi ga majalisar dokokin kasar ya haura kashi 70 cikin 100 na Naira biliyan 197 da shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa ‘yan majalisar a kudurin kasafin kudin da ya mika wa majalisar.
SERAP ta ce, “Kasafin kudin majalisar dokokin kasar na Naira biliyan 344.48, wanda ya kai kusan Naira biliyan 147, an ruwaito shi ne kasafin mafi girma da aka taba gudanarwa a majalisar.
Wannan ci gaban ya zo ne yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, makonni biyu da suka gabata, ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2024 na Naira tiriliyan 28.7.
Ku tuna cewa ‘yan majalisar sun tara kasafin Naira tiriliyan 27.5 na shekarar 2024 da Shugaba Tinubu ya gabatar zuwa Naira tiril
iyan 28.7.
