Connect with us

News

Asalin yadda aka samo sunan Hausa Bakwai da Banza Bakwai

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Wasu sun san garuruwan da ake kira ‘Hausa Bakwai’ da ‘Banza Bakwai’ amma ba su san dalilin da ya sa ake kiransu da waxannan sunayen ba. Wannan ne ya sa naga dacewar yin wannan dan takaitaccen bayanin kamar yadda na tava karantawa a littafin ‘Kano Ta Dabo Cigari’ na Marigayi Wazirin Kano Alhaji Abubakar.

Bayan Bayajidda ya gudo daga kasar Borno shi da matarsa mai suna Magaram saboda yunkurin kashe shi da Sarkin (Shehu) Borno ya yi, sai suka zo wani gari da ake kira Garun Gabas a kasar Hadeja. A nan ya bar matarsa saboda tsohon cikin da take dauke da shi ya wuce Daura.

Advertisement

Yanzu-yanzu: Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Roma ta raba gari da kocinta Jose Mourinho

Bayan ya isa Daura cikin dare, ya sauka a gidan wata tsohuwa, sai ya nemi ruwa amma bai samu ba. Tsohuwar take fada masa dalilin da ya sa basa samun ruwa sai sau daya a sati saboda wata macijiya da take hana dibar ruwan.

Da Bayajidda yaji haka, sai ya karbi guga a wajen tsohuwar, ya nufi rijiyar Kusugu inda macijiyar take ciki, ya kashe ta ya debi ruwa. Da gari ya waye, Sarauniya Kabara (wacce take mulkin Daura) ta ji labari, sai ta sa aka yi bincike aka gano Bayajidda ne ya kashe macijiyar.

Advertisement

 

Ta kirasa ta ce, za ta basa rabin mulkinta. Amma ya ki amincewa, ya ce mata sai dai a daura musu aure da ita idan ta amince. Sarauniya ta yarda, aka daura musu aure da Bayajidda. Sai jama’ar garin suka fara kiransa da ‘Makas-Sarki.’ Daga baya kuma suka koma ce masa ‘Sarki’ kawai. To daga nan ne aka samo kalmar Sarki da ake fadawa wasu sarakuna a yau. Da Sarauniya Kabara ta haifi da namiji, sai aka sanyawa yaron suna Bawo.

Advertisement

A lokacin da Bawo yake mulkin Daura, an yi wata masifaffiyar yunwa a kasar Hausa, wacce ta zama babu inda ake samun abincin mai yalwa sai a wani wuri wanda shi ne Kano a yanzu. Don haka kabilu suka rika kaura zuwa wurare masu dan yalwan abinci domin su tsira da rayuwarsu.

Bayan jama’a sun fita kowa ya samu in da ya fake, sai ya zamana babu shugabanci kowa zaman kansa yake. Daga nan sai zalunci ya yawaita a tsakanin jama’a. Masu karfi su kwace kayan raunana. Wannan ne ya sa raunana suka fara kai kukansu Daura wajen Sarkin Bawo.

Advertisement

Da kararraki suka yawaita, sai Sarki Bawo ya yi shawarar kafa shuwagabanci a dukan waxannan wuraren da abin ya dama. Sai ya tura dansa Bagauda zuwa Kano, ya tura dansa Gunguma zuwa Zariya, ya tura dansa Duma zuwa Gobir, ya tura dansa Kumayo zuwa Katsina, ya bawa dansa Gazori rikon Daura, ya bawa dansa Zamna Biram, ya tura dansa Kogo zuwa Rano. Wadannan garuruwa da Sarki Bawa ya bawa ‘ya’yansa ko ya tura su, su ake kiran Hausa Bakwai.

Akwai kuma Banza Bakwai, wanda Sarki Bawo ya sake tura wasu ‘ya’yan nasa bakwai zuwa can. Sai dai kuma wasu masana sun ce ba ‘ya’yansa na cikinsa ba ne, ‘ya’yan dan uwansa mai suna Karaf-da-gari ne wanda Bayajidda ya haifa da wata baiwarsa mai suna Bagwariya.

Advertisement

Wadannan garuruwa bakwai da aka tura ‘ya’yan su ne: Zamfara da Gwari da Nupe da Yaruba (ilori) da Kwarrafa da Kebbi da Yawuri. Su ne ake kira Banza Bakwai.

Wannan shi ne asalin yadda aka samo sunan ‘Hausa Bakwai’ da kuma ‘Banza Bakwai’.

Advertisement

Mohammed Bala Garba, Maiduguri.

Dalibi daga jami’ar Tarayya ta Maidiguri (Unimald). 0809833126

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending