Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya za ta fara bai wa ɗalibai lamuni – Ministan Ilmi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa a cikin Janairu za ta fara sakin kuɗaɗen lamuni ga ɗalibai.

Ministan Ilmi Yusuf Sununu ne ya bayyana haka, tare da cewa har yanzu maganar fara biyan a cikin watan Janairu ma na nan.

Ma’aikatan Lafiya: Za Mu Hukunta Duk Wanda Aka Samu DaLaifi  – Dr. Nagod

Sununu ya ce tuni ma an fitar da manhaja ta yanar gizo, inda dukkan ɗalibin da ke buƙatar lamunin zai shiga ya cika fam, matsawar ya cika sharuɗɗan da ake buƙata.

 

Ya ce shirin bayar da lamunin ya nan domin akwai shi a cikin kasafin 2024.

Advertisement

 

Sannan kuma ya ce Majalisar Zartaswa ta amince a kafa rassan makarantun wasu ƙasashen waje a nan Najeriya, domin a ƙara samun yawan ɗalibai masu shiga jami’o’i da yawa.

 

Ya ce hakan kuma zai zaburar da manyan makarantu da cibiyoyi wajen yawan yin bincike-binciken faɗaɗawa da zurfafa ilmi.

 

Wannan shiri dai an bijiro da shi ne domin rage wa ɗalibai raɗaɗin tsadar rayuwa, biyo bayan cire tallafin fetur, wanda haifar da tsadar abinci, kayan masarufi da tsadar zirga-zirgar sufuri baki ɗaya.

Advertisement

 

Yayin da gwamnatin tarayya ta yi wa ma’aikata ƙarin Naira 30,000 tsawon watanni huɗu zuwa shida, su kuma ɗaliban manyan makarantu za a ba su bashi domin rage barazanar matsalar rayuwa da kuma kuɗaɗen makaranta.

 

Sai dai kuma za a bada lamunin ne ga ɗaliban da suka fito daga gidajen masu iyaye masu ƙaramin ƙarfi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending