Connect with us

News

Kanawa Na Farin Ciki Kan Nasarar Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf A Kotun Koli – Muhammad Zahraddin

Published

on

Manajan Darakta na kamfanin Yakam Multimedia Muhammad Muhammad Zahraddin

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Manajan Darakta na kamfanin Yakam Multimedia Muhammad Muhammad Zahraddin na taya murnar nasarar da Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya samu a kotun ƙoli.

Advertisement

Muhammad ya ruwaito cewa Maza da mata da sun fito kan titunan Kano domin murnar hukuncin da kotun koli ta yanke na ayyana gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben gwamnan jihar.

Gwamnatin Legas ta haramta sayarwa da amfani da robar ‘take-away’

Kanawa sun yi dafifi a tituna jihar, suna rera wakoki, kade-kade da raye-raye don nuna farin cikinsu.

Advertisement

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa idan dai za a iya tunawa an gwabza kazamin a dawa tsakanin jam’iyyar adawa ta APC da kuma jam’iyyar NNPP mai mulki a fafutukar da ta ke yi na karbar kujera mafi daraja a jihar, inda a yau kotun koli ta mayar da ita ga jam’iyyar NNPP bayan ta sha kashi sau biyu a kotun sauraron kararrakin zabe da kotun daukaka kara a jere.

Muhammad ya nuna farin cikinsa da cewa, wannan ba karamar nasara Bace. Gwamna ya cancanci yabo, saboda ya kawo ci gaba Mai yawa da kuma shugabanci nagari ta hanyar shimfida ayyukan da jama’a ke bukata ba tare da la’akari da munanan kalubalen da lamarin ya jawo a jihar ba, ya kara da cewa hakan ya nuna gwamna yana da zuciya mai kyau tare da mayar da lamuransa ga Allah

Advertisement

Muhammad ya ci gaba da cewa wannan nasara ta al’ummar jihar Kano ce da aka kusa kwace wa hakkinsu, haka kuma nasara ce ta Nijeriya da dimokuradiyya saboda an tabbatar da hukuncin da ‘yan kasa suka yanke, wanda shi ne manufa ta tsarin mulkin dimokuradiyya a duk fadin duniya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending