News
Gwamnatin Legas ta haramta sayarwa da amfani da robar ‘take-away’
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kwana kaɗan bayan Gwamnatin Jihar Legas ta kafa dokar hana sarrafawa, sayarwa da zuba abinci cikin robar ‘take-away’, yanzu haka an bayar da umarnin a damƙe duk wanda aka ƙara gani ya na sayar da robar ta zuba abinci.
Haka umarnin ya haɗa da duk wanda ya zuba wa kwastomomi abinci a cikin robar da kuma wanda ya sayi abinci aka zuba masa a ciki.
Yan Majalisar Filato Da Kotu Ta Kwace Kujerunsu Sun Lashi Takobin Dowawa Bakin Ai
Sanarwar ta fara ne da bada umarnin a garƙame duk wata masana’antar da aka yin robobin na zuba abinci da kuma manyan dillalan da ke sayarwa lodi-lodi.
Premium Times ta ruwaito cewa Kwamishinan Tsaftace Muhalli na Jihar Legas, Tokumbo Wahab ne ya sanya wa sanarwar hannu da kan sa, a wata takardar da aka fitar ranar Lahadi.
Sanarwar ta umarci Hukumar Tsaftace Jihar Legas, wato LAWMA da Dakarun Yaƙi da Rashin Ɗa’a su gaggauta su fara damƙe duk wanda ya karya wannan doka.
Wahab ya ce abin takaici ne ƙwarai yadda waɗannan robobi suka cushe magudanun ruwa, sannan kuma a kullum gwamnati na asarar maƙudan kuɗaɗe wajen yashe magudanan ruwan.
Ya ce mafi yawan sharar da jami’an LAWMA ke fama da ita kan tituna da gefen titinan a kullum, duk robobin abinci ne na ‘take-away’.
Ya ce daga yau Gwamnatin Jihar Legas ba za ta zuba ido ya riƙa zubar da ƙazanta ba, sannan a bar ta da kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tsaftace gari.
