Connect with us

News

An Tsige Kunle Oluomo Daga Mukaminsa Na  Shugabancin Majalisar Dokoki

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta tsige Shugabanta, Kunle Oluomo, daga kan mukaminsa.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa sha takwas (18) daga cikin mambobin majalisar 26 suka kada kuri’ar tsige Mr. Oluomo a yayin zamanta na ranar Talata.

Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Kwamitin Sa ido Kan Tsaro A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna

An tsige Mr. Oluomo ne a bisa zarginsa da wawure kudade da rashin jin shawara da wasu laifuffukan masu nasaba da wadannan.

Advertisement

Nan take Majalisar ta zabi wani mamba mai suna, Oludaisisi Elemide, ya maye gurbinsa a matsayin sabon shugaba.

A jawabinsa na farko tun bayan dambarwar tsigewar, sabon Shugaban majalisar ya bukaci samun kwanciyar hankali tsakanin mambobinta.

Advertisement

Ya kara da cewar, sabanin yadda wasu ke rade-radi, ba’a tsige tsohon shugaban majalisar ne domin yakar gwamnan jihar Dapo Abiodun ba.

Ya ci gaba da cewar, al’amarin na cikin damar da Kundin Tsarin Mulki Kasa ya baiwa ‘yan majalisar na zaben wanda suke so ya jagorancesu.

Advertisement

Daga bisani majalisar ta dage zamanta tsawon makonni 2, inda sandar girman majalisar ta kasance a hannun sabon Shugaban a matsayin wata alama ta jagoranci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending