Connect with us

News

Ba Mu Kama Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Ba – Hukumar DSS

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta ce bata kama shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo ba, sabanin rahotannin da ake yadawa.

Da yake amsa tambayoyi, mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya ce “Bello Bodejo ba ya tare da DSS.”

Advertisement

Mayakan Boko Haram  Sun Kashe Hafsan Soji Sun Kwace Sansanin Sojoji A Borno

An kama Bodejo ne a ranar Talata a babban ofishin Miyetti Allah a Tundun Maliya a Babban Titin Abuja zuwa Keffi a Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa.

Mutane da dama sun yi tsokaci a shafukan sada zumunta, cewa ana kyautata zaton jami’an DSS ne, suka kama shugaban da yammacin ranar Talata.

Advertisement

An kama Bodejo ne saboda fargabar kan kirkiro kungiyar ‘yan banga ta Nomad wadda ka iya haifar da tashin hankali a nan gaba.

Ana zargin kungiyar ba ta da rajista da jami’an tsaro, wanda yake wani sharadi da ake bukata kafin kafa wani abu da ya shafi tsaro a Nijeriya.

Advertisement

Leadership ta ruwaito cewa ayan kafa kungiyar ‘yan banga, Bodejo ya jaddada cewa ‘yan bangar za su bi dokokin kasar nan a lokacin gudanar da ayyukansu.

Bodejo, yayin da yake jawabi yayin kaddamar da ‘yan bangar a garin Lafia na jihar Nasarawa, ya bukaci ‘yan sa-kan da su hada kai da ‘yansanda, sojoji, da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a fadin kananan hukumomi 13 na jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending