Connect with us

News

Mayakan Boko Haram  Sun Kashe Hafsan Soji Sun Kwace Sansanin Sojoji A Borno

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO

 

Mayakan Boko Haram sun kashe wani hafsan soja da wasu ’yan sa-kai biyu a wani ƙazamin hari a sansanin sojoji a Jihar Borno.

Wata majiyar soji ta shaida Jaridar Aminiya  cewa an kasa ɗauko gawar waɗanda aka kashe, saboda tsananin faɗan da aka gwabza da misalin ƙarfe 1 na dare a sansanin da ke yankin Krenowa a Ƙaramar Hukumar Marte ranar Asabar.

AFCON 2023: Ghana Ta Kori Koci Da ’Yan Tawagar Horas Da ’Yan Wasanta Bayan Cire Su

Ta ƙara da cewa maharan sun lalata wata motar yaƙi, amma direbanta ya tsira da rauni a ƙafarsa, sannan sojoji fiye da 100 tare da makamai da sauran kayan aikinsu sun janye zuwa garin Marte.

Ƙoƙarinmu na jin ta bakin kakakin Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa, Manjo-Janar Edward Buba, ya faskara.

Advertisement

Mun kira wayarsa amma ba ta shiga, sannan har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoton ba mu samu amsar rubutaccen saƙon da aka tura masa ba.

Amma wasu majiyoyi sun shaida mana cewa mayaƙan Boko Haram sun kai wa sojojin hari ne kwanaki biyar bayan sojojin sun ƙwace sansanin ƙungiyar da ke Krenowa a ƙoƙarin sojojin na kakkaɓe ’yan ta’adda.

Wani soja ya shaida wa wakilinmu cewa, “mun kai musu hari muka ƙwace sansaninsu, amma daga baya suka kawo mana harin kwanton ɓauna, dole muka janye.

“Ina kyautata zaton ɓuya suka yi, saboda babu wata alamar shirin harin kwanton ɓauna.

“A ƙarshe dai sansanin rundunar 27 Task Force da ke garin Marte muka koma,” in ji majiyar sojin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending