Connect with us

News

Harin Tudun Biri: Nan Da Makonni Biyu Za A Fara Sake Gina Sabon Garin Tudun Biri – Uba Sani

Published

on

Gwamna jihar Kaduna, Sanata Uba Sani

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Gwamna jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa, nan da makonni biyu masu zuwa, za a fara sake gina garin Tudun Biri da wani jirgin soja mara matuki ya jefa wa Bam a ranar 3 ga watan Disamba, 2023.

Advertisement

Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Asabar din da ta gabata yayin da yake jawabi a wajen taron kwamitin zartarwa da ayyuka na kasa na kungiyar Fityanul Islam ta Nijeriya, wanda aka gudanar a jami’ar jihar Kaduna.

Ba mu da masaniya kan ficewar Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso – Ecowas

Gwamnan Uba Sani ya yi alkawarin bayar da filayen gina Jami’ar da kungiyar Fityanul Islam ta Nijeriya ke shirin yi.

Advertisement

Leadership ta ruwaito cewa da yake mayar da martani ga kalaman jagoran kungiyar Musulunci ta kasa wanda tun farko a jawabinsa ya bukaci a gaggauta cika alkawuran da aka dauka wa al’ummar Tudun Biri, Gwamna Sani ya ce, ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kwanaki biyar da suka gabata kan alkawurran da gwamnatin tarayya ta dauka na sake gina garin Tudun Biri.

Ya ba da tabbacin cewa, za a gina gidaje, asibiti, makaranta, kasuwa da ofishin ‘yansanda a garin a karkashin aikin sake gina Tudun Biri da Gwamnatin Tarayya za ta yi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending