News
Hukumar NDLEA Ta Kama Mata 15 Da Ake Zargi Da Fataucin Miyagun Kwayoyi A Kano.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano, ta kama wasu mutane 198 da ake zargi da hannu a laifuka daban-daban da suka shafi muggan kwayoyi a ci gaba da gudanar da aikin Operation Hana Maye
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar NDLEA reshen jihar Kano ASN II Sadiq Muhammad Maigatari ya fitar.
Ya ce an gudanar da aikin ne domin yakar shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi a jihar.
Ya ci gaba da cewa, kokarin da rundunar ta yi ba tare da bata lokaci ba ya sa an kama mutane da dama, ciki har da fasa gidajen miyagun kwayoyi da kuma kwato haramtattun abubuwa.
“A yayin gudanar da aikin “Operation Hana Maye” da aka kaddamar a ranar 17 ga watan Junairu 2024, hukumar NDLEA ta Kano ta yi nasarar cafke jimillar mutane 198 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban. Musamman ma, a cikin wadanda aka kama akwai mutum 61 da ake zargi, ciki har da mata 15 da aka kama a wani kulob da aka rikide zuwa hada-hadar miyagun kwayoyi.”
Bugu da kari, ya ci gaba da cewa, rundunar NDLEA ta Kano ta kama wasu mutane 42 da ake zargi a makabartar Dan Agundi.
Maigatari ya bayyana cewa, aikin ya kuma tarwatsa gidajen shan magani a makabartar Sheka da sheka Obajana.
Ya kara da cewa, “Wadannan kame-kamen sun hada da kwayoyi daban-daban kamar Exol – 5, maganin roba, tsotsa da mutu, cannabis, da sauran abubuwa masu haɗari.
