News
Ministan Makamashi ya bayyana dalilan sa na ƙara samun taɓarɓarewar wutar lantarki a Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Najeriya ta danganta ƙara taɓarɓarwar wutar lantarki a ƙasar nan da dalilan rashin samun wadataccen gas ga kamfanonin samar da wuta wato, GenCos.
Ministan Makamashi Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwar da ya wallafa a shafin sa X, a jiya juma,a
“Jiya mun zauna da kamfanonin samar da wuta, wato Gencos, domin lalubo hanyoyin da za mu magance yawan ɗauke wuta a wasu sassan ƙasar nan.
An samu ƙarin wutar lantarki a lokacin Kirsimeti da Sabuwar Shekara, sai dai kuma abin takaici an samu koma-baya a cikin sabuwar shekara.
“Bayan mun gudanar da bincike, sai muka gano cewa rashin samun wutar wadatacciya na da alaƙa da ƙarancin gas ga kamfanonin da ke samar da wutar,” inji ministan.
Yayin da ake fama da matsalar ƙarancin wutar lantarki, har yau masu biyan kuɗin wutar lantarki a Najeriya ba su kai mutum miliyan 12 ba, kamar yadda wani binciken da NBS ya gudanar ya nuna.
Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa, NBS ta bayyana cewa yawan masu biyan kuɗin wutar lantarki ya ƙaru da mutum 240,000 a tsakiyar 2023, inda adadin yawan ya tashi daga miliyan 11.47 zuwa miliyan 11.71.
Wannan ƙididdiga dai ta na nufin har yanzu masu biyan kuɗin wutar lantarki ba su kai mutum miliyan 12 har zuwa ƙarshen 2023 ba.
A ranar Alhamis NBS ta fitar da wannan ƙididdiga a Abuja, mai nuna cewa daga watannin tsakiyar 2023 zuwa watannin kusa da na ƙarshen 2023 an samu ƙarin masu biyan kuɗin wutar lantarki da kaso 2.08 bisa 100.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an yi wannan ƙididdigar bisa ma’aunin yawan bila-bilan biyan kuɗin wutar lantarki, yawan kuɗaɗen shigar da aka samu a watannin da kuma ƙididdigar yawan kwastomomin kamfanonin sayar da wutar lantarki, wato Discos.
Rahoton ya ce an samu ƙarin yawan masu biyan kuɗin wutar lantarki idan aka kwatanta da yawan su a Disamba ɗin 2022, inda a lokacin mutum miliyan 10.94 ne.
Hakan na nuni da cewa an samu ƙarin yawan mutum har kashi 7.09 bisa 100 kenan, daga Disamba 2022 zuwa Disamba 2023.
