Connect with us

News

Gamayyar Kungiyar Matasan Fulani FUYAN Ta Yi Kira Da A Saki Bello Bodejo 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Kungiyar matasan ta Najeriya mai suna Fulani Youth Association of Nigeria (FUYAN) ta koka akan ci gaba da tsare Alhaji Dr Abdullahi Bello Bodejo, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Wanda ta ke raya al’adun Fulani a kasa.

A cikin Sanarwar da ta aikewa manema labarai a ranar juma’a da safe ta hannun mai Magana da yawun ta kuma jami’in hulda da jama’a na kungiyar Miyetti Allah na kasa Ambasada Muhammad Tasi’u Sulaiman (FUYAN) ta ce cigaba da tsare Alhaji Dr Abdullahi Bello bodejo da sojojin Najeriya ke yi ba bisa ka’ida ba ne.

An Haifi Yara ‘Yan Biyu Maza A Hade

A faɗin ( FUYAN) sojoji ba su da iko a bisa dokar ƙasa su tsare ko wanne mutum Fiye da awa ashirin da huɗu (24h) kuma kungiyar tana kira da babban murya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga Lamarin a bada umarnin sakin shi da gaggawa.

Sun ce shugaban Miyyetti Allah Kautal Hore an ɗauke shi ne a ofishin sa da ke tudun Wada a karamar hukumar Karu da ke jihar Nassarawa, kuma an tsare shi a hannun Sojojin Najeriya a Asokoro da ke birnin tarayya Abuja.

Advertisement

Sojojin a Najeriya ba a ba su iko, a dokan kasa su tsare ko wanne ɗan ƙasa ba . Jami’an ƴan sanda da DSS su ne kaɗai aka ba iko su tsare mutum.Tsare Alhaji Dr Abdullahi Bello bodejo na tsawon lokacin nan ba bisa Ƙa’ida ba ne.

Ya kamata Sojojin su miƙa shugaban zuwa ga ƴan sandan Najeriya ko kuma su ba DSS, takardan ko wanne irin bincike da su ke masa akan wannan abin da ba bisa ka’ida ba, sojojin sun tsare shi ba tare da ikon kundin tsarin aiki ba.

Muna kira ga shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta ba da umarni a saki Dr Abdullahi Bello bodejo.

Sojojin Najeriya ba su da ikon tsare ko wanne mutum fi ye da awa ashirin da huɗu (24h) ba tare da an Kai shi kotu ba. Saboda haka tsare shugaban Mu Alhaji Dr Abdullahi Bello bodejo ya saɓawa doka ko kuma ya zama sabo a kan dokar ƙasar Najeriya, a faɗin (FUYAN.)

Malam Sulaiman ya roƙi mambobin wannan ƙungiyar da shuwagabannin ta da su cigaba da natsuwa da bin doka kamar yadda su ke jiran sakin shugaban su.

Cigaba da tsare Alhaji Dr Abdullahi Bello bodejo da sojojin Najeriya ke yi ba tare da an kai shi kotu ba. Shugaban matasan Fulani ya ce: wannan ƙarfin ikon su ne, wanda sojojin su ke ganin ba wanda ya isa ya hukunta su kuma lauyoyun su na nan suna shiri akan wannan al’amarin.

Advertisement

Idan sojojin Najeriya na da wani hujja a kan Dr Abdullahi Bello bodejo, akan laifin da ya yi wanda doka ta sani a kaishi kotu ya fi tsare shi da aka yi ba bisa Ƙa’ida ba domin wannan ya saɓawa yancin ɗan adam da ke zayyane a dokokin ƙasa.

Hukumomin jami’an tsaron Najeriya Wanda aka san su da korewa akan girmama dokokin ƙasa da nuna ɗabi’o’i da aka san su da shi, a yi amfani da su ta wajen sakin Bello bodejo kamar yadda dokar ƙasa ta bashi iko a matsayin ɗan ƙasa mai bin doka da odar Najeriya, kuma a barshi ya taho gida, yadda ake cigaba da tsare shi ba bisa ka’ida ba ne kuma ba bisa dokar ƙasa ba ne

Alhaji Dr Abdullahi Bello bodejo an tsare shi ne kwananan a maƙasudin ƙaddamar da yan sa kai mai suna Nomad vigilantee Group a Lafia hedkwatar jihar Nassarawa a ranar 17 ga watan Janairu 2024 wanda ya biyo bayan ce-ce-kucen jama’a a kasa.

Alhaji Dr Abdullahi Bello bodejo ya ce,. Maƙasudin manufofin kafa Wannan yan sa kai don a taimaka wajen tsare rayukan manoma da makiyaya kuma da taimakawa wajen tattaro bayanan sirri ga hukumomin tsaron Najeriya daga munafukai da yan ta’adda daga ƙauyuka kuma da bunƙasa zaman lafiya a ƙauyukan mu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending