Connect with us

News

INEC ta Bayyana Sakamakon Yan Majalisun Jihar Kano Guda biyu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana dan takarar jam’iyyar NNPP , Alhassan Ishaq, a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Kura/Garun Mallam a jihar Kano.

Rashin tsaro: ka magance ta’addanci ko ka yi murabus  – Ƴan Najeriya ga Gwamnatin Tarayya

Baturen zaben na INEC Farfesa Shehu Galadanchi ya bayyana cewa Ishaq na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 37,262 inda ya doke Hayatu Musa Daurawa sallau na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 30,803.

Idan dai za a iya tunawa kotun daukaka kara ce ta umarci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfuna 20 na mazabar Kura/Garun Malam a jihar Kano.

Advertisement

Haka kuma, INEC ta ayyana Bello Butu-Butu na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Rimin Gado/Tofa.

Babban Baturen zaben Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ya sanar da cewa Bello Butu-Butu na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 31,135 inda ya doke abokin takararsa na APC wanda ya samu kuri’u 25,577.

Kotun daukaka kara ta kuma umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 33 a mazabar Rimin Gado/Tofa dake jihar kano.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending