News
Yan bindiga sun sako ɗalibai da malaman jihar Ekiti da suka sace
DAGA IDRIS USSAINI NGURU
An sako ɗalibai da malaman makarantar ‘Apostolic Faith Montessori’ da ke jihar Ekiti da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su ranar Litinin da ta gabata.
INEC ta Bayyana Sakamakon Yan Majalisun Jihar Kano Guda biyu
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Sunday Abutu, ya tabbatar da sakin ɗaliban tare da malamansu cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Sai dai kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce maharan sun kashe tare da ƙona gawar direban motar ɗaliban a lokacin da suke hannunsu.
An dai sace ɗaliban da malaman nasu ne a lokacin da suke dawowa daga wata tafiya da suka yi.
Dalibai biyar ne da malamansu uku da kuma direban motar ne ke cikin motar a lokacin da aka sace su.
Sun kuma shafe kusan kwanaki bakwai a hannun ‘yan bindigar da suka sace su.
Cikin wata sanarwar da ta fitar, gwamnatin jihar ta tabbatar da sakin ɗaliban tare da malamansu.
Sanarwar ta kuma ambato gwamnan jihar Biodun Oyebanji na gode wa shugaban ƙasar Bola Tinubu kan goyon bayan da ya bayar wanda shi ne ya taimaka har aka kai ga sakin mutanen.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
