News
An Karrama Masu Fasahar Zane Zane Wato “Art” Da Kyautuka Domin Karfafa Masu Gwiwa Wanda Herwa Heart Of Art Initiative
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An karrama masu fasahar zane zane wato “Art” da kyautuka domin Karfafa masu gwiwa wanda HERWA HEART OF ART INITIATIVE ta Jagoranta karkashin Shugaba Ambassador Hon. Hajja Khaltume Gana
Professor Aliyu Muhammad na Jami’ar Ahmad Bello Zaria Masanin Ilimin Zane Zane yajagoranci raba kyautukan yakuma ja hankalin dalibai dama al’umma game da baiwar da su ke da ita yacce yana da kyau suke amfani da ita wajen bunkasar cigaban najeriya.
Tsadar Kayan Abinci: Gwamna Abba Kabir Yusuf Zai Nemi Taimakon Shugaba Tinubu
Kiran hakan yazo ne a yayin gudanar da karrama wasu dalibai da sukai hazaka a ofishin Herwa Heart of Art Initiative da ke a unguwar Tarauni Jihar Kano
Prof. Aliyu Muhammad na Jami’ar Ahmad Bello Zaria yacigaba da cewa zane “Art” wani fanni ne na dogaro dakai yacigaba da cewa ya godewa Allah da malamansa da suka dorashi a wannan fanni na zane na Art wanda yace duk wani abu da bawan Allah yakesamu na rayuwar duniya dai dai gwargwado Allah ba abinda bai mallakamasa
Prof. Aliyu Yakuma yi kira da babbar murya cewa a cigaba da karfafawa yaranmu gwiwa domin koyan wannan sanaa na Art koyo ba lallai sai anshiga ajiba cudanya da akeyi awaje sanaar shima wani fanni ne na koyan Art domin koyan waje yafi na cikin aji.
Daga karshe Prof. Aliyu Muhammad Ya yabawa Hajja Khaltume Gana bisa kokarinta na karfafar Matasa masu Art Yakuma bawa dalibai kyautuka da Certificate da sukai kwazo haka kuma cikin wadan suka halarci taron akwai Kachalla Kutumbawa Comrade Dahiru Muhammad Maihula wanda shima yasaka albarka a taron ya raba kyautuka na certificate ga kungiyoyi duk ayayin taron Manyan Baki Sunhada da Doctor RN Aminu Shehu Ishaq
Herwa Heart of Art Initiative sunkware wajen bawa dalibai da kananan yara horo a fannin Ilimin Zane Zane wato Art amatakin koyo Kala Kala
