Connect with us

Sports

Najeriya ta yi wajerod da Afirka ta Kudu a bugun fenareti, kuma ta kai wasan ƙarshe.

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Najeriya ta samu nasarar zuwa wasan ƙarshe a gasar cin koin ƙwallon ƙafa na nahiyar Afirka, 2023 da ke gudana a Ivory Coast.

Najeriyar ta kai wasan na ƙarshe ne bayan ta doke Afirka ta Kudu a bugun fanareti da ci 4-2.

Kashi 50 Bisa 100 Na Magungunan Da Ake Shigo Da Su Najeriya Duk Jabu Ne Kuma Masu Haɗarin Gaske – Hukumar NAFDAC

A yanzu Najeriya za ta kara da duk ƙasar da ta yi nasara a karawar da ake yi yanzu haka tsakanin mai masaukin baƙi Cote d’Ivore da Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo.

An je bugun fanareti ne a wasan Najeriya da Afirka ta Kudu ne bayan kwashe minti 120 ana fafata wasa ba tare da an samu ƙasar da ta zura ƙwallaye mafi yawa ba.

Inda aka tashi wasan Najeriya na da ƙwallo ɗaya, Afirka ta Kudu ma tana da ƙwallo ɗaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending