Connect with us

Sports

Gwamnatin jihar Kaduna ta ɗauki nauyin nuna wasan Najeriya a wasu wurare

Published

on

Daga Muhammad Muhammad Zahraddin

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ɗauki nauyin nuna wasan ƙarshe na Kofin Afirka na (Afcon) da Najeriya za ta fafata da ƙasar ivory Coast mai masaukin baƙin gasar a yau Lahadi da maraice.

Hukumar NDLEA ta kama mutum 92, muggan kwayoyi masu nauyin kilogiram 217 a Kaduna

Cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan kafofin yaɗa labarai na zamani, Abdallah Yunus Abdallah ya wallafa a shafinsa na X ya ce za a nuna wasan a waɗansu wasu manyan makarantun jihar.

Wuraren da za a nuna wasan kyauta sun haɗar ta wuraren nuna wasanni na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da jami’ar jihar Kaduna, da Kwalejin fasaha ta KASU da Kwalejin ilimi na Gidan Waya da Kwalejin gwamnatin tarayya ta Zariya.

Tuni dai shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar shugaban ƙasa zuwa wasan ƙarshen.

Advertisement

Najeriya na fatan lashe kofin na Afirka karo na huɗu a tarihi, idan ta yi nasara a kan Ivory Coast.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending