Sports
Kwaddebuwa Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirka Bayan Ta Ci Najeriya 2-1
Masaukin Bakin gasar kofin nahiyar Afirka ta bana, Kwaddebuwa, ta lashe gasar bayan ta ci Najeriya 2-1 a wasan karshe na AFCON
Najeriya ne ta fara zura kwallo bayan da mai tsaron baya, Williams Troost Ekong ya farke saura minti 7 kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Ama minti 63, masaukin bakin suka rama, inda Franck Kessie ya zura wa Kwaddebuwa.
Najeriya ta canja dan wansan tsakiya nan Samuel Chuwkueze da Moses Simon a minti na 56 sannan Kwaddebuwa ta canja ‘yan wasa biyu.
Stephane Singo ya karbi Serge Aurier sannan Max Gradel ya maye gurbin Oumar Diakite a baya da tsakiya.
Sai dai a miniti na 81 Sebastien Haller ya zura kwallo na biyu wa masaukin bakin.
Najeriya ta sake sauya ‘yan wasantaa minti na 86, a yayin da Joe Aribo ya maye gurbin Zaidu Sanusi, Terem Moffi ma ya maye gurbin Frank Onyeka a karawar a minti na 86.
Kwaddebuwan ta yi nasara ne bayan an kara akalla minti 8 a wasan, inda aka tashi ci 2-1
Advertisements
-
News7 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News3 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
