Connect with us

News

Direbobin dakon mai a Najeriya sun yi barazanar fara yajin aiki daga Litinin

Published

on

DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA

 

A Najeriya, ana iya sake fuskantar karancin man fetur, sakamakon alwashin da kungiyar masu motocin haya ta sha na dakatar da dakon man daga ranar Litinin mai zuwa saboda tsadar gudanar da ayyukansu.

Kungiyar ta sha yin korafi a kan matsanancin tsadar man diesel da ‘yayanta ke amfani da shi wajen aikin dakon man fetur zuwa sassan kasar.

DA ƊUMI-ƊUMI: Kungiyar kwadago ta sanar da yin zanga-zangar a fadin Nijeriya

a halin da ake ciki, ana sayar da duk litar man diesel a kan kudi da ya kai tsakanin naira dubu 1 da dari 2 da 50 zuwa dubu daya da 400 – ya danganta da yankin da ake saye.

A wata sanarwa da ya fitar a Abuja babban birnin Najeriya, shugaban kungiyar masu motocin hayar, Yusuf Othman ya ce lalai ‘yayan kungiyar za su ajiye motocinsu daga ranar Litinin ta maako mai zuwa.

Advertisement

Othman ya ce hakan ya zama wajibi ne duba da cewa ‘yayan kungiyar na taafka asara a aikin dakon man da suke yi, saboda haka ba za su iya ci gaba da jurewa ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending