News
Gwamnatin Jihar Kano zata fara hukunta iyayen da basa tura yaran,su makaranta
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano ta yi barazanar daukar kwararan matakai a kan iyayen da suke sakaci da karatun ‘ya’yansu
Kwamishinan Ilimi Umar Doguwa ne ya yi wannan gargadin yayin wani taron masu ruwa da tsaki da suka yi da mata kan “mahimmancin ilimin ‘ya’ya mata domin bunkasa zamantakewa da tattalin arziki” a jihar Kano
Doguwa ya ce gwamnatin,su ba zata laminci rashin zuwan makaranta, da yara kanana keyiba Kuma zasu hukunta duk wani mahaifin da yake barin yayan,sa na yawo akan a tituna a lokacin makaranta kamar Yadda daily post ta rawaito
Kwamishinan Ya ce shiyasa gwamnatin jihar Kano ta mayar da ilimi kyauta, kamar yadda ta samar da hanyoyin jigilar yara zuwa makarantu, da dai sauran
Adan haka muke baiwa iyaiyaye shawara su kara kaimi da Kuma rubanya kokarin da sukeyi sun tura ya,yansu makaranta
Munaso ace Yara suna amfani da irin kayayyakin aikin koyo da koyarwar da gwamnatin mu ta Samar a cewar Kwamishinan
Ya ce, “Lokacin da muka hau, mulki mun Sami harkar ilimi a cikin wani hali mai ban tausayi
mun,sami dalibai miliyan 5.3 a jihar, Amman 4.5 a zaune suke daukar darasi babu abin Zama
.
“Gwamnatin da ta gabata ta rufe makarantun kwana 28. Kuma Muna da dalibai sama da 32,000 a cikin makarantun Amman yanzu Sama da 9,000 basa zuwa makaranta
Adan haka gwamnatin mu karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware kashi 29.7 na kasafin kudi domin biyan albashi ga malaman makaranta
